Zargin wawure kudaden jami'a a Niger

Wata takaddama ta kunno kai a jami'ar Abdulmumini Dioffo dake jamhuriyar Niger, bisa zargin yin almundahana da tsabar kudi CFA biliyan Daya da Miliyan Dari shida.

Wani karamin mai ajiyar kudi ne a jami'ar ake zargin ya rinka ciro wannan kudi a asusun jami'ar har na tsawon shekaru Biyar.

Sai dai hukumomi a jami'ar sun nisanta kansu da salwantar wannan kudi.

Wannan al'amari dai ya kai kungiyar daliban jami'ar ta ABDU mumuni Dioffo ta Yamai din ga kira ga gwamnatin Alhaji Mahamadou ISSOUFOU da ta gudanarda wani bincike mai zurfi a kan wannan matsala.