EFCC ta yi yunkurin kama Bankole

Dimeji Bankole
Image caption Dimeji Bankole an cikin tsaka mai wuya

A Najeriya Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati, wato EFCC, ta yi yunkurin kame Kakin Majalisar Wakilai mai barin gado, Hon. Dimeji Bankole.

Sai dai al'amarin ya kai ga sa-in-sa tsakanin jami'an hukumar da kuma jami'an da ke tsaron lafiyar Kakakin Majlisar.

Hukumar ta EFCC dai ta gayyaci Hon. Bankole ne ya bayyana a gabanta don ya wanke kansa daga zarge-zargen da ake masa na karkatar wasu kudaden Majalisar ta Wakilai, gayyatar da bai amsa ba.

Na hannun damansa dai sun ce kakakin Majalisar bai amsa gayyatar ba ne saboda hukumar ta EFCC ba ta bi hanyoyin da suka dace ba wajen mika bukatar tata.

Yunkurin na jami'an hukumar ta EFCC bai yi nasara ba ne saboda turjewar da jami'an 'yan sanda da na hukumar tsaro ta farin kaya, wato SSS wadanda ke tsaron lafiyarsa suka yi.

'yan sanda ne suka shiga tsakani

Wata majiya a ofishin hukumar ta EFCC wadda ba ta so a ambaci sunanta ba, ta tabbatarwa BBC cewa jami'an hukumar sun yi yunkurin kama Hon Bankole ne bayan ya ki amsa gayyatar da suka yi masa a lokuta daban daban don ya amsa tambayoyi dangane da wasu zarge-zarge.

Majiyar ta kuma kara da cewa isar jami'an hukumar gidan Hon Bankole ta zo a kan gaba domin a daidai wannan lokacin ne kakakin majalisar mai barin gado ya ke shirin ficewa zuwa kasashen waje.

Sai dai a cewar majiyar, rundunar 'yan sanda ta kasa ta shiga tsakani, inda ta nemi jami'an hukumar ta EFCC su saurarawa Hon Bankole har sai ya mika ragamar shugabancin majalisar wakilan.

To amma 'yan sandan sun ki tabbatar da hakan.

Rahotanni sun ambato wasu na hannun damansa suna cewa hukumar ta EFCC ba ta bi hanyoyin da suka dace ba don gayyatar Hon Dimeji Bankole, amma majiyar hukumar ta ce an bi duk matakan da suka dace a sharia'nce.

Hukumar ta EFCC dai ta bukaci Hon Bankole ya bayyana a gabanta ne dangane da zargin sarrafa kudaden Majalisar Wakilai da kuma yin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar ta EFCC ta ce tana so ne Hon Bankole ya yi mata bayani a kan wasu kudade da suka kai naira biliyan goma, wadanda aka ce an karbo rance da sunan Majalisar ba tare da sanin sauran 'yan majalisa ba, al'amarin da ya jawo cecekuce a majalisar.

Ana kuma zargin Hon Bankole da hannu a karkatar da wasu kudade daga kasafin kudin Majalisar da kuma kari a kan farashin wasu motoci da aka sayawa shugabannin majalisar a shekarar 2008.