Ina fama da matsananciyar rashin lafiya - Mladic

Ratko Mladic a kotu
Image caption Ratko Mladic shi ne mutumin da aka fi nema ruwa a jallo a Turai

Tsohon kwamandan dakarun Bosnia Ratko Mladic, ya gayawa kotun hukunta laifukan yaki ta duniya a Hague cewa yana fama da matsananciyar rashin lafiya.

Janar Mladic ya yi kalaman ne bayan da ya bayyana agaban kotun a karon farko.

Janar din dai na fuskantar zargin aikata laifukan yaki ne a lokacin rikicin Bosnia shekaru 19 da suka wuce.

A wancan lokaci dai, dakarun Bosnia sun kashe musulmai kusan dubu takwas, abinda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta sha alwashin sai an hukunta duk wanda ke da hannu a ciki.

Janar Mladic ya ce yana bukatar lokaci domin fahimtar laifukan da ake zarginsa da aikatawa. An dai dage zaman kotun zuwa farkon watan Yuli.

Shi ne kusan mutum na karshe a cikin jeren wadanda kotun ta Hague ke nema ruwa a jallo.