Nijar ta jaddada neman makamashin nukiliya

Ma'aikatan nukiliya na IAEA Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnati ta yi watsi da damuwar 'yan adawa

Gwamnatin jUmhuriyar Nijer ta mayar da martani game da damuwar da kungiyoyin kare muhalli ke nunawa a kasar game da shirin gwamnatin Nijar din na kafa tashar nukiliya.

Gwamnatin Nijer ta bayyana cewa kasancewar Nijer daya daga cikin kasashe dake kan gaba wajen samar da ma'adanin yuraniyam bai kamata a ce jama'ar kasarta na zaune ba tare da wutar lantarki ba.

Malam Marou Amadou shi ne ministan shari'a kuma kakakin gwamnatin Nijar ya ce kasar za ta so ta dauki hanyoyin da wasu ke ganin su ne suka fi, amma kuma ba masu sauki ba ne.

Ya kuma ce shiri ne na tsawon lokaci da ba yau za a zartar da shi ba, ba kuma gobe ba.