An kai hari fadar shugaban Yemen

Abdallah Saleh Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Abdallah Saleh na fuskantar matsin lamba

An harba rokoki akalla biyu da suka dira a harabar fadar shugaban kasar Yemen dake babban birnin kasar Sana'a. Inda rahotanni ke cewa shugaban ya samu rauni.

Wani kakakin gwamnati ya shaida wa BBC cewa, harin rokokin ya shafi masallacin dake fadar shugaban kasar, kuma mutane uku sun jikkata.

Wasu rahotanni sun ce Shugaba Saleh ya samu dan karamin rauni, yayin da mataimakin Fira Minista da kakkin Majalisar dokokin kasar su ma suka samu raunuka.

Amma jami'an gwamnatin sun ki cewa uffan kan wadannan bayanai.

Wannan dai shi ne ya mutsi na baya-bayan nan yayin da fada ke ci gaba da kazanta a birnin Sana'a, tsakanin dakarun shugaba Saleh, da kuma kabilun da suka dau makamai.

Wakiliyar BBC tace: tuni dai Amurka ta tura wakili yankin da nufin lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin na Yemen.

Amma kuma masu sa ido akan al'amuran kasar na ganin da wuya shugaba Saleh ya sauka daga kan karagar mulki.