Majalisar wakilan Najeriya ta wanke Patricia Etteh

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar wakilan Najeriyar ta wanke tsohuwar kakakin Majalisar, Honourable Patricia Etteh, akan duk wasu zarge-zargen aikata cin hanci da rashawa.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne a zaman da ta yi na karshe a jiya, gabannin kafa sabuwar Majalisar dokokin kasar da za'a yi a ranar litinin mai zuwa.

Ita dai Honourable Patricia Etteh, ta rike mukamin kakakin Majalisar ne a baya, daga bisani kuma ta sauka daga kan mukamin nata, bayan ta fuskanci matsin lamba daga akasarin 'yan Majalisun, wadanda suka bukace ta data sauka, ko kuma su tsige ta.

A wancan lokacin ana zarginta da ware wasu makudan kudade don bada kwangilar gyaran gidan da aka tanadarwa kakakin majalisar.