Matakan samar da tsaro a Nigeria

Rundunar 'yan sandan Najeriya, reshen jahar Rivers, ta bullo da sabbin matakan shawo kan harin bama-bamai a yankin.

Jahar ta Rivers da wasu jihohin yankin na Niger Delta dai suna fama da hare-haren da ake dangantawa da masu ikirarin kwato wa yankin hakkokinsa.

Rundunar 'yan sandan ta Rivers ta ce, daga cikin dubarun da zata yi amfani da su a nan gaba, har da karnuka na musamman.