A yau za'a gudanar da zaben yan Majalisar dokoki na Portugal

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban jam'iyyar yan adawa Pedro Coello

A yau ne al'ummar kasar Portugal zasu kada kuri'arsu a babban zaben kasar.

Wasu batutuwa da suka yi kane-kane a yakin neman zabe sun hada da yiwuwar zaftare irin kudaden da gwamnati take kashewa da kuma kara kudin haraji da aka tsara a matsayin wani sharadi na baiwa kasar tallafin kudi.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta nuna za'a fafata tsakanin jam'iyyar dake mulki ta 'yan gurguzu da kuma ta 'yan adawa wato centre right social democrats, duk da cewar binciken baya bayannan ya nuna cewar jam'iyyar adawar, ita ke kan gaba.

Wani wakilin BBC ya ce duk jam'iyyar da ta sami nasara, zata fuskanci tarin kalubale iri iri,na ganin an gudanar da wasu sauye sauye da jama'a basa son ganin anyi.

Shugaban yan adawa, Pedro Passo Coelho ya ce zai dau mataki a wasu wurare fiye da yadda yarjejeniyar bashin da suka cimma da asusun bada lamuni na duniya ke bukata.

Sai dai jam'iyyar Socialists me mulki na zarginsa da nuna kosawarsa na mika wasu ma'aikatun gwamnati masu muhimanci ga kamfanoni masu zaman kansu.