An wuce da shugaba Saleh kasar Saudiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a kasar Yemen

Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh ya bar kasar zuwa Saudiya domin neman magani.

Ya iso Saudiyar da tsakar dare ta jirgin sama daga birnin Sana'a tare da wasu jami'an gwamnatin da suka samu raunuka sakamakon harin rokar da aka kai a ranar juma'a a harabar gidan shugaban kasar.

Mr Saleh zai samu magani akan konewar da ya yi da kuma ciwon da ya samu a kasan zuciyarsa.

Sai dai wasu na ganin watakila shugaban wanda a lokuta da dama ya dau alkawarin sauka daga mulki ba zai dawowa ba.

Mr saleh ya yi ta fuskantar matsin lamba daya sauka daga kan kujerar mulki.

Kuma wani wakilin BBC yace tafiyar tasa ka iya raunana matsayinsa.

Jami'an gwamnatin kasar sun zargi mayakan kabilun kasar da kuma 'yan adawa da cewar su suka kai hari a gidan shugaban kasar,amma sun musanta wannan zargi.