A yau za'a fitar da sakamakon barkewar cutar E-coli

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu jinya a asibiti

Jami'an kasar jamus sunce a yau ne suke tsammanin tabbaci game da musabbabin barkewar nau'in kwayar cutar nan ta E Coli da ya zuwa yanzu ta hallaka mutane ashirin da biyu, da kuma illata daruruwan wasu jama'a.

A ranar lahadi ne dai hukumomi suka ce sun gano alamun dake nuna cewar cutar ta samo asali ne daga nau'in waken da aka shuka a Uelzen, me nisan kilomita dari da kudancin Hamburg.

Hukumomin sun fada wa jama'a cewa kada su kuskura su ci nau'in waken na sprouts.

Sun kuma ce suna duba batun ko akwai sauran abincin da suka gurbace me yuwa a wata kasuwa ko gona.

Watakila a samu tambayoyi dangane da dalilin da yasa aka dora ma gonakin Spain laifi tun farko a lokacin barkewar annobar,alhalin kuwa musababbin cutar na kusa da gida ne .

Sai dai yayinda a yanzu an gano musabbabin barkewar annobar ana sa ran za'a samu raguwa a adadin mutane dake kamuwa da rashin lafiya .