Gwajin sabon adreshin intanet IPv6

Gwajin sabon adreshin intanet IPv6  Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Adreshin Ipv4 zai ci gaba da kasancewa har nan da shekaru goma,

Manyan kamfanonin intanet sun fara gudanar da gwaji mafi girma kan adreshin IP samfuri na shida.

Kamfanonin Google da Yahoo da Microsoft Bing da kuma Facebook na daga cikin kamfanonin da ke gwada wannan samfuri na shida a shafukansu na intanet domin gwajin rana daya.

Ana bullo da fasahar ne a hankali saboda fasahar samfuri na hudu da ake amfani da ita ta fara tsufa, gannin yadda ake samun karuwar abubuwan da ake durawa a intanet.

Kamfanoni da masu amfani da intanet a gida na bukatar sabbin na'urori, sai dai sauyin ka iya daukar shekaru.

Ranar da aka ware ta tsandaurin shiga intanet samfuri na shida - rana ce kawai ta kamfanonin intanet ke gwada yadda fasahar ke aiki, da kuma kara wayar da kan jama'a.

Sabbin kayan aiki

Ga jama'a kalilan din da ke amfani wannan samfuri na 6, za su shiga intanet ta adreshin da suka saba - kamar Google.com ko Yahoo.com.

A bayan fage, mabincikar bayanansu za ta maida su kan sabuwar fasahar.

Kungiyoyin da abin ya shafa sun ce a hankali kowa zai sauya daga adreshin IP na hudu zuwa na shida, amma kada mutane su damu idan ba su sauya yanzu ba.

"Shafukan intanet za su ci gaba da aiki, amma za a dakatar da duk wasu sauye-sauye da tallafi gare su nan gaba," a cewar Philip Sheldrake mamba a kungiyar sa kai dake wayar da kai kan sabon adreshin na IPv6 a Burtaniya.

Kasuwanci ya kare

Komawa amfani adreshin IP na 6 na da 'yar wahala ga kamfanonin da ke amfani da intanet.

Sauya fasalin kwamfiyutocinsu domin su dace da samfurin zai hadar da sanya sabbin na'urori.

Ga masu amfani da intanet a gida kuwa, wannan abune kamar yadda aka saba sauya na'ura ko gyara ta.

"Sai dai an bar kamfanoni a baya sosai," a cewar Sebastien Lahtinen na Thinkbroadband.com.

Sai dai Mr Lahtinen ya ce ya kamata shugabannin wadannan kamfanoni su gane cewa wannan sauyin na nan tafe don haka akwai bukatar su shiryawa rungumarsa.

Duk da cewa adreshin Ipv4 zai ci gaba da kasancewa har nan da shekaru goma, akwai alfanu a sauyin, a cewar Philip Sheldrake.

"Akwai bukatar yin wannan sauyin. Yana da mahimmanci a yi shi yanzu maimakon nan gaba, hakan zai nuna cewa suna tafiya da zamani, kuma za a gansu tsaf a fagen intanet na zamani."