Mark ya sake zama shugaban Majalisar Dattawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar Dokokin Najeriya

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, David Mark, ya sake darewa kujerar shugabancin Majalisar, bayan da mambobin Majalisar suka zabe shi a Jamhuriya ta Bakwai.

Mista Mark ne kadai ya tsaya neman kujerar.

Zaben nasa ya zo daidai da tsarin jam'iyyar PDP, wadda ta ware kujerar ga shiyyar Arewa Maso Tsakiya a kasar, inda Mista Mark ya fito.

Mista Mark ya dawo Majalisar ne a karo na hudu, bayan ya lashe zabe a mazabar sa a Jihar Benue a watan Afrilu.

Har wa yau dai an zabi Ike Ekweremadu, wanda mataimaki ne ga Mista Mark a baya, a matsayin mataimakin shugaban majalisar.