Hukumar EFCC ta kama tsohon kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Image caption Tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati a Nigeria wato EFCC, tace ta kama tsohon kakakin Majalisar wakilan kasar Dimeji Bankole a daren ranar lahadi.

Kakakin hukumar Femi Baba Femi ya tabatarwa BBC da kamen kuma ya ce an kama Mr Bankole ne da misalin karfe takwas na daren jiya a gidansa dake anguwar asokoro a Abuja .

Hukumar ta kuma ce akwai zarge-zarge masu yawa da ake yimasa na yin zamba, da suka hada da batun sayen motoci akan kudi fiye da naira biliyan biyu, inda ake zarginsa da karkatar da wani kaso daga cikin kudaden.

Ana kuma zarginsa da yin sama da fadi da kasafin kudin da aka ware wa majlisar a bara da yawansu ya kai naira biliyan tara.

Hukumar EFCCn ta ce zargin baya bayanan shine na yin sama da fadi da kudaden da yawansu ya kai naira biliyan ashirin da biyar, inda naira biliyan goma sha biyar daga ciki, na kasafin kudin da aka ware wa majalisar ne yayinda naira biliyan goma na bashin da aka karba daga wurin bakunan kasar ne.

Ta ce ta dau wanan mataki ne sakamakon bayanan sirri da ta samu akan cewa Mr Bankole na shirin tserewa daga kasar ta bayan fage.

Kamen dai na zuwa ne gabanin akawarin da tsohon kakakin Majalisar wakilan yayi na bayyana a gaban hukumar domin amsa wasu tambayoyi, dangane da zarge zargen da ake yi masa.

Yinkurin kama shi

A makon da ya gabata ma, Hukumar ta EFCC, ta yi yunkurin kame Kakin Majalisar.

Sai dai al'amarin ya kai ga sa-in-sa tsakanin jami'an hukumar da kuma jami'an da ke tsaron lafiyar Kakakin Majlisar.

Hukumar ta EFCC dai ta gayyaci Hon. Bankole ne ya bayyana a gabanta don ya wanke kansa daga zarge-zargen da ake masa na karkatar wasu kudaden Majalisar ta Wakilai, gayyatar da bai amsa ba.

Na hannun damansa dai sun ce kakakin Majalisar bai amsa gayyatar ba ne saboda hukumar ta EFCC ba ta bi hanyoyin da suka dace ba wajen mika bukatar tata.

Yunkurin na jami'an hukumar ta EFCC bai yi nasara ba ne saboda turjewar da jami'an 'yan sanda da na hukumar tsaro ta farin kaya, wato SSS wadanda ke tsaron lafiyarsa suka yi.

'yan sanda ne suka shiga tsakani

Wata majiya a ofishin hukumar ta EFCC wadda ba ta so a ambaci sunanta ba, ta tabbatarwa BBC cewa jami'an hukumar sun yi yunkurin kama Hon Bankole ne bayan ya ki amsa gayyatar da suka yi masa a lokuta daban daban don ya amsa tambayoyi dangane da wasu zarge-zarge.

Majiyar ta kuma kara da cewa isar jami'an hukumar gidan Hon Bankole ta zo a kan gaba domin a daidai wannan lokacin ne kakakin majalisar mai barin gado ya ke shirin ficewa zuwa kasashen waje.

Sai dai a cewar majiyar, rundunar 'yan sanda ta kasa ta shiga tsakani, inda ta nemi jami'an hukumar ta EFCC su saurarawa Hon Bankole har sai ya mika ragamar shugabancin majalisar wakilan.

To amma 'yan sandan sun ki tabbatar da hakan.

Rahotanni sun ambato wasu na hannun damansa suna cewa hukumar ta EFCC ba ta bi hanyoyin da suka dace ba don gayyatar Hon Dimeji Bankole, amma majiyar hukumar ta ce an bi duk matakan da suka dace a sharia'nce.