China na kokarin sasanta rikicin Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption NATO ta kaddanar da hare-hare sau dubu goma akan dakarun Kanal Gaddafi

Jiragen Nato na ci gaba da kai hari a babban birinin Libya Tripoli. Wadanda suka gani da ido sun ce an ji kararar tashin bamai-bamai kusa da gidan Kanal Gaddafi.

NATO dai ta ce ta kaddamar da hare-hare akan dakarun Kanal Gaddafi fiye da sau dubu goma a Libya.

Kasar China da Rasha dai na shirya wani taron diplomasiyya domin kawo karshen rikicin Libya.

Ministan kasashen wajen Libya Abdulati Al-Obeidi zai ziyarci Beijing sai kuma jakadan Rasha Mikhail Margelov wanda ya ziyarci Benghazi,yana tattaunawa da 'yan tawaye.