An dakile yunkurin 'yan tawaye a Zawiyya

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan tawayen Libya

Gwamnatin Libya ta ce ta dakile wani sabon yunkuri da 'yan tawaye suka yi na kwace garin Zawiyya da ke yammacin kasar.

'Yan tawayen sun ce an tafka kazamin fada a tsakiyar garin, amma 'yan jaridar da aka kai garin sun ce alamu sun nuna cewa hankali na kwance kuma yana karkashin ikon gwamnati.

A watan Maris ne dai dakarun gwamnati suka sake kwace garin, wanda ke da tazarar kilomita talatin yamma da birnin Tripoli, bayan an kwashe kwanaki biyu ana gwabza fada.

Kakakin gwamnatin ta Libya, Moussa Ibrahim ya ce rahotannin son zuciyar da wadansu 'yan jarida suka bayar cewa 'yan tawaye na kara samun nasara ba gaskiya ba ne.

A cewar Mista Ibrahim ba a yi wani fada mai tsanani ba a garin.

"Bayan 'yar musayar wuta da sojoji ta 'yan sa'o'i aka fatattaki 'yan tawayen", in ji Mista Ibrahim, wanda ya kara da cewa an yiwa 'yan tawaye kusan dari kawanya a wajen garin.

Mai magana da yawun 'yan tawayen, M'hamed Ezzawi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an gwabza kazamin fada.

"Dakarun sojin (na Libya) na amfani da manyan makamai--sun fi 'yan tawaye makamai. Ya zuwa yanzu ba mu da adadin wadanda suka yi shahada, amma akwai akalla mutane bakwai da aka yi wa rauni a tsakanin 'yan tawayen.

Kwace iko da Zawiya dai zai ba 'yan tawayen damar samun muhimmiyar hanyar shigo da kayayyaki daga Tunisia.libya