Gaddafi: Ba mu da wani zabi

Gidan talabijin din Libiya ya watsa wani sako na muryar Kanar Gaddafi, inda yake cewa zai cigaba da kasancewa a birnin Tripoli, ko a raye ko a mace.

Kanar Gaddafin ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su taru a harabar gidansa.

Hakan na faruwa ne, awoyi bayan da kungiyar tsaron NATO ta kai daya daga cikin hare-hare mafi muni a birnin Tripoli da rana tsaka, tun bayan da ta kaddamar da farmaki a kasar.

Jiragen saman NATO masu tashi kasa-kasa sun kai hare hare fiye da 20 a yau.