Za'a samu ambaliyar ruwa a Niger bana

Hukumomin Nijar sun gargadi 'yan kasar dangane da hasashen samun ambaliyar ruwa a kasar.

A kwanan nan ne hukumar binciken yanayi ta kasa ta yi hasashen cewa, za a sami ruwan sama sosai a daminar bana, wanda har zai iya haddasa ambaliyar ruwa.

Gwamnatin Niger din dai ta yi kira ga manoma da su guji kasancewa a cikin yankunan da ke cikin kwari ko a magudanan ruwa.

Gwamnatin ta kuma ce ta tanadi wani asusu domin tinkarar duk wani bala'i irin na ambaliyar ruwa.

A kasar ta Niger dai dubban mutane ne suka rasa muhalli, yayinda wasu suka rasa rayukansu a damanar bara, sakamakon ambaliyar ruwa.