PDP ta yi tir da zaben kakakin majalisa

Kakakin jam'iyyar PDP
Image caption Kakakin jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta nuna damuwarta matuka game da yadda zaben shugabbani majalisar wakilai Nijeriya ya gudana.

Jam'iyyar dai ta nanata muhimmancin dake tattare da tsarin karba karba, wanda ta ce har yanzu yana kunshe a kundin tsarin mulkinta.

A jiya ne dai majalisar wakilan da sa kafa ta shure tsarin karba-karbar na jam'iyyar PDP inda ta zabi Hon Aminu Waziru Tambuwal a matsayin akakin majlisar da kuma Emeka Ihedioha a matsayin mataimakinsa.