Mazauna Jisr al-Shughur a Syria na dar dar

syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga zanga a Syria

Al'ummar kasar Syria mazauna garin Jisr al-Shughur sunce suna fargabar za ayi mummunar zubar da jini idan hukumomi suka aiwatar da barazanarsu na tabbatar da doka da oda a garin.

An buga wannan sanarwar ta fargaba ce a wani shafin Intanet mai adawa da gwamnati bayan kafofin yada labaran kasar sun bada rahoton cewar wasu kungiyoyin masu dauke da makamai sun kashe akalla jami'an tsaro dari da ashirin.

Shafin Intanet din dake goyon bayan 'yan adawa ya yi Allah Wadai da hasarar rayukan da aka yi, amma kuma masu zanga zanga sun karyata zargin gwamnati na cewar kungiyoyin mutanen dake dauke da makamai ne suka kashe jami'an tsaron.

Wani dan rajin kare hakkin bil adama a Syria Wissam Tarif ya shaidawa BBC cewar duka laifin ya rataya ne akan gwamnati

Yace "babu wani tashin hankali da makamai. Ana zanga zangar lumana ne kawai. Duk inda kaga makamai to gwamnati ne ke amfani dasu".

Sai dai a daya bangaren, kakakin ma'aikatar yada labaran Syria Reem Haddad ta ce jami'an tsaro ba sa kaiwa fararen hula hari, face wadanda ke dauke makamai.

Haddad tace "ba zan saka su cikin jerin fararen hula ba saboda fararen hula basa daukar makamai. Kamar ta'adanci ne ke faruwa a can. Gaskiyar magana kenan. Wadannan jami'an tsaron sun mutu ga gawarwakinsu nan. Kuma suna da iyalai da 'ya'ya. Abinda ke faruwa kenan a can".

A halin yanzu ana cikin wani yanayi mai rikitarwa don tantance asalin lamarin dake aukuwa a Jisr al-Shughur.