Jama'a na tserewa daga garin Jisr al-Shugr a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga Arewa maso Yammacin Syria sun ce jama'a na tserewa daga garin Jisr al- Shugur inda hukumomin kasar suka ce 'yan bindiga masu tada kayar baya sun hallaka jami'an tsaro dari da ashirin a jiya Litinin.

Gwamnatin Syriar dai ta sha alwashin cewa za ta yi amfani da karfi wajen maido da doka da oda a garin.

Wasu karin rahotanin sun ce an ga kai da kawon sojojin gwamnati a yankin.