Ana ci gaba da gwabza fada a Yemen

Jami'an tsaro a yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A kalla an kashe mutane dari tun da aka fara rikici a Yemen

Ana ci gaba da tafka kazamin fada a kudancin kasar Yemen, kwanaki kadan bayan shugaban kasar Ali Abdallah Saleh ya tafi kasar Saudiyya domin yin jinya.

Akalla mutane goma sha biyar sun rasu sakamakon wani mummunan batakashi a garin Zinjibar tsakanin dakarun gwamnati da kuma wasu wadanda jami'an gwamnati suka ce 'yan Alqaeda ne.

Bugu da kari kuma hukumomin kasar sun bayar da sanarwar cewa shugaba Ali Abdallah Saleh zai dawo kasar nan da makwanni biyu daga kasar Saudiyya inda yake shan magani.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce mika mulki ba tare da bata lokaci ba shine mafi a'ala ga al'ummar kasar Yemen.

Amurka da Saudi Arabiya suna matsin lamba na kokarin ganin an sauya mulki a Yemen a dai dai lokacin da Shugaba Ali Abdallah Saleh baya cikin kasar.

Amurka ta yi kira da a gudanarda sauyin gwamnati cikin ruwan sanyi a Yemen.