Gargadi kan tattalin arzikin Afghanistan

Sojojin kawance a Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin kawance a Afghanistan

Wani kwamiti mai fada-a-ji na majalisar dattawan Amirka yayi gargadin cewa, akwai yiwuwar Afghanistan za ta fuskanci mummunan koma bayan tattalin arziki, bayan janyewar dakarun kasashen waje daga kasar, a shekara ta 2014

A cikin wani rahoto da ya kalli tasirin agajin da Amirka ta baiwa Afghanistan din, wanda ya kusa kai dala biliyan goma sha tara, senatocin sun yanke hukuncin cewa, an sami sakamakon da ya sabawa juna - musamman a yankunan da aka fi fafatawa da 'yan Taliban.

Suka ce dole tun yanzu a soma shiri, idan ana son kaucewa matsalar tattalin arziki a AFghanistan din.