Birtaniya da Faransa na matsa kaimi kan Syria

hague Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague

Birtaniya da Faransa suna matsa kaimi don ganin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar yin Allah wadai da gwamnatin Syria saboda yadda ta ke murkushe masu adawa da ita.

Jami'an diflomasiyya sun yi wa takardar da za a mikawa Kwamitin garanbawul don ya kunshi damuwar wadanda ke adawa da matakin na Birtaniya da Faransa.

Sakataren harkokin wajen Faransa, Alain Juppe, ya ce bai dace ba a ce Kwamitin Sulhun ya yi shiru a kan tashin hankalin da ke kara munana a kasar ta Syria.

Takardar kiran a dauki mataki a kan Syria ya yi Allah wadai da tashin hankalin kuma ya bukaci a kawo karshen bude wuta ba tare da bata lokaci ba.

Sabanin matakin da aka dauka a kan Libya, a wannan karon ba za a yi amfani da karfin soji ba don kare fararen hula ko kuma kakabawa Syria takunkumi.

Amma dai wadansu wakilan Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya kamar su Brazil da Afirka ta Kudu da India na fargabar cewa wannan matakin farko ne na daukar irin matakin da aka dauka a kan Libya,kuma ba su ji dadin yadda NATO ke ta barin wuta ba saboda a tunaninsu an wuce gona da iri.

A kan haka ne kuma kasashen Birtaniya da Faransa suka yiwa takardar da za su mika garanbawul don ya kunshi ra'ayin wadannan kasashen kamar yadda jami'an diflomasiyya suka bayyana.

Manufar ita ce don Birtaniya da Faransa su samu goyon bayan da ya dace don kar Rasha da China su samu galaba don kuwa suna adawa da duk wani mataki a kan Syria.