EFCC ta gurfanar da Bankole a gaban kotu

Dimeji Bankole Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dimeji Bankole

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon-kasa, EFCC, ta gurfanar da tsohon kakakin Majalisar Wakilan kasar, Dimeji Bankole, a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin ya aikata jerin laifuka goma sha shida.

Mai shari'a Donatus Okorowo ne dai ya jagoranci zaman kotun, kuma lauyan hukumar ta EFCC ne, Festus Keyamo, ya fara karanta jerin zarge-zargen da hukumar ke yi wa Mista Bankole da wadansu mutanen jerin tuhumce-tuhumcen, wadanda suka shafi zargin kashe kudin majalisar sama da naira miliyan dubu goma sha daya ba bisa ka'ida ba.

Ana dai zargin an kashe kudin ne a kan wadansu hidimomi wadanda suka hada da sayen akwatunan talabijin da na'urorin kwamfuta da kuma wadansu motoci.

Sai dai tsohon kakakin Majalisar Wakilan bai amince da zarge-zargen ba.

Lauyan hukumar ta EFCC ya nemi a kara wa hukumar lokaci ta hanyar tura sauraron karar zuwa gaba domin ya samu damar kammala bincike don shigar da wadansu karin zarge-zargen.

Ganin haka ne lauyan da ke tsayawa wa tsohon kakakin ya nemi a bayar da belin sa duk kuwa da cewa bai sanya bukatar a cikin jerin martanin da ya gabatar wa kotu a rubuce ba, bukatar da lauyan EFCC ya ki amincewa da ita.

Daga nan sai alkalin kotun ya raba gardama, inda ya bukaci bangarori biyun su sake bayyana a gaban kotu ranar Juma'a mai zuwa don bai wa lauyan tsohon kakakin damar gabatar da bukatar belin a rubuce.

A sannan ne kuma kotu za ta duba yiwuwar ba da belin.

Amma lauyan na EFCC ya ce da wuya ya amince ko da an gabatar da bukatar belin a rubuce.

Bayan an kammala zaman, lauyan na EFCC ya shaida wa BBC dalilin da ya sa ya ke dadi-dari da maganar bayar da belin tsohon kakakin.

"Muna da hujjar da za mu kafa cewar ba mutum ne da kan so ya je gaban shari'a cikin dadin rai ba; ko dabi'ar da ya nuna lokacin da aka je kama shi ta isa abin misali game da yadda yake gudun shari'a".

Hukumar ta EFCC dai, a karar da ta shigar, ta ce tana tuhumar tsohon kakakin ne da wadansu mutanen, to amma lauyan ta ya ce da zarar lokaci ya yi za su sanar da duniya ko su wanene wannan maganar ta shafa.

Dangane da ikirarin hukumar EFCC cewa tana da sauran zarge-zargen da za ta gabatar wa kotu lauyan tsohon kakakin, Afolabi Fashano, cewa ya yi:

"A shirye muke mu kare tsohon kakakin game da wadannan zarge-zargen ko ma wadansu da za su taso.

"Ba na son wuce makadi da rawa dangane da hukuncin da kotu za ta yi nan gaba, amma ba zai hana ni cewa a shirye muke ba".

Kotun dai ta kebe ranakun ashirin da shida da kuma ashirin da bakwai na watan Yulin wannan shekarar don fara sauraron karar gadan-gadan.

Sabanin irin yanayin da hukumar EFCC ta kame tsohon kakakin ranar Lahadin ta wuce inda ta iza keyarsa zuwa ofishinta yana sanye da wata karamar riga mai gajeren hannu da wando turoza, a wannan karon tsohon kakakin ya samu sanya irin fararen tufafin da aka san shi da su daga sama har kasa, kuma ba sarka ko ankwa a hannayensa, sai dai an yi masa zobe da jami'an tsaro masu yawan gaske dauke da makamai, kana aka girke wadansu a ciki da wajen harabar kotun, amma hakan bai hana wadansu matasa shiga da wadansu takardu dauke da rubuce-rubucen da ke neman a saki tsohon kakakin ba.