Obama ya yi watsi da ikirarin Majalisa

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaba Obama na Amurka ya yi watsi da ikirarin da 'yan Majalisar Dokokin kasar suka yi cewa yana bukatar amincewarsu kafin ya ci gaba da shigar da sojojin Amurka cikin rikicin Libya.

Da ma dai Kakakin Majalisar Wakilai John Boehner ya yi gargadin cewa gwamnatin Obama ta kusa keta wa'adin kwanaki sittin da doka ta baiwa shugaban kasar ya nemi amincewar majalisa kafin ci gaba da daukar matakin soji.

Sai dai jami'an fadar gwamnatin Amurka ta White House sun ce rawar da sojojin Amurka ke takawa a Libya takaitacciya ce—hakan kuma na nufin ba lallai ne gwamnatin ta bukaci amincewar majalisa ba.

Tuni dai wadansu 'yan Majalisar Dokokin su goma suka garzaya kotu inda suka shigar da kara suna zargin Shugaba Obama da keta dokar da ta bukaci shugaban kasar ya nemi amincewar Majalisa cikin kwanaki sittin da daukar matakin soji.

Daya daga cikin 'yan majalisar da suka shigar da karar, Roscoe Bartlett, ya shaidawa BBC dalilansu na zuwa kotun:

“Dalilai uku ne kacal za su sa shugaban kasa ya shigar da sojojin mu cikin wani al'amari: na farko shi ne idan muka kaddamar da yaki a kan wata kasa; na biyu, idan muka ba shi amincewar Majalisa, na uku kuma idan aka kawo mana hari ko kuma idan akwai kulle-kullen kawo mana hari.

“Babu daya cikin wadannan dalilai da ya faru, saboda haka daga lokacin da ya kaddamar da yaki a Libya, Shugaba Obama ya keta tanade-tanaden Dokokin Yaki na Kasa”.

Dan majalisar ya kuma yi gargadin cewa wannan mataki da Shugaba Obama ya dauka ba tare da samun amincewar Majalisa ba ka iya zama mummunan abin koyi.

A halin da ake ciki kuma yau Alhamis ne ake sa ran wani jami’in diflomasiyyar Rasha zai gana da gwamnatin Libya a birnin Tripoli, a wani yunkuri na shiga tsakani a rikicin da ke faruwa a can.

A makon da ya gabata ne dai Mikhail Margelov ya gana da wakilan ’yan adawa a birnin Benghazi.

Gwamnatin Kanar Gaddafi dai ta ce ba za ta amince da tsagaita wuta da kuma tattaunawar siyasa ba, har sai ’yan adawar sun amince da cewa shugaban zai ci gaba da kasancewa a kan mulki, al’amarin da kungiyar tsaro ta NATO ta ce sam ba za ta sabu ba.

Karin bayani