NATO za ta ci gaba da luguden wuta a Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya ce kungiyar za ta ci gaba da kai hare hare a kan Libya har sai ta murkushe dakarun Kanar Gaddafi.

Mista Rasmussen ya ce tilas ne kawancen ya shirya kasancewa a kasar bayan Kanar Gaddafi, amma NATO ba za ta sa dakarunta a kasa ba domin tabbatar da doka da oda bayan an kawo karshen rikicin.

Mista Rasmussen na magana ne a karshen taron ministocin tsaro na kasashen NATO, wanda aka yi a Brussels domin duba sakamakon hare-haren da kungiyar ke kaiwa ta sama a Libya.