NATO na nazari akan Luguden wuta a Libya

nato Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yadda NATO ke barin wuta a Libya

Ministocin tsaro na kasashen NATO zasu yi taro a Brussels don sake nazarin luguden wuta ta sama da suka shafe fiye da watanni biyu suna yi a Libya a yayinda suka kara azama a matakinsu na soji.

An ji fashashen a daren jiya a Tripoli babban birnin kasar bayan shafe yinin jiya ana wurga bam bamai. Shugaban Libya Kanar Gaddafi ya ce zai cigaba da zama a Libya a mace ko a raye.

Mako guda daya wuce ne NATO ta amince a cigaba da barin wuta a Libya har na karin kwanaki casa'in. Tun wancan lokacin kwamandojinta sun maida hankali ne akan kar hari babu kakkautawa ta sama .

Taron ministocin na ranar Laraba zai maida hankali ne akan cewar a cigaba da matsin lamba kada a daga kafa. Ita sai NATO na ganin cewar sojojin Kanar Gaddafi dabararsu ta kare kuma babu wanda ya san lokacin da gwamnatin Gaddafin zata ruguje.

Sai dai kakakin gwamnatin Libya Moussa Ibrahim yace sojojin NATO sun kashe fararren hulu babu iyaka inda yace suna goyon bayan bangaren da baida jama'a basa so.

Yace"gwamnatocin yammaci suna maida hankali akan haka. Kuna goyon bayan bangaren da baida karfi. Haramtaccen bangaren da jama'a basa so. Idan har zaman lafiya koken son gani a Libya ku goyi bayan mu ba 'yan tawaye ba".

Ita dai kungiyar NATO na kokarin tattaunawar gaggawa akan batun gwamnatin rikon kwarya da kuma kalubalen da za ayi fusakanta akan batun fararen hula da kuma batun tsaron kasar.

Kuma taron na Brussels da wuya ya dauki mataki akan batun rawar da NATO zata dauka bayan kamalla yakin a Libya.