Wasu kungiyoyin manoma da makiyaya sun koka a Nijar

Taswirar Jumhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijar

A Nijar, wasu kungiyoyin makiyaya da manoma na kukan cewa, hukumomi na mayar da su saniyar ware, a shirye shiryen tinkarar daminar ba.

Kungiyoyin sun kuma yi kira ga hukumomin da su sa ido sosai domin tabbatar da cewa an kiyaye dokokin da suka shafi kare filayen noma da na kiwo - ko Burtulla.

A jiya ne mahukuntan Nijar din suka ce sun tanadar wa manoma isashen taki, bayan da hukumar kula da yanayi ta kasar ta hango cewa, a bana za a sami ruwan sama mai yawa, har ma zaa iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa kamar yadda aka samu a bara.