'Akwai rikicin kabilanci a Kudancin Sudan'

Wadansu mutanen Kudancin Sudan
Image caption Wadansu mutanen Kudancin Sudan

Wani sabon rahoto a kan Sudan ya ce bambance-bambancen kabila a Kudancin Sudan ka iya kaiwa ga karuwar tashe-tashen hankula, ya kuma yi barazana ga zaman lafiyar yankin, wanda kwanan nan zai zama sabuwar kasa a nahiyar Afirka.

Da ma dai alamu kalilan ne ke nuna cewa darewar kasar Sudan za ta faru cikin ruwan sanyi.

Dangantaka tsakanin arewaci da kudanci ta yi tsami matuka yayin da ake ci gaba da fafatawa a Jihar Kudancin Kordofan.

Sai dai a cikin yankin Kudancin Sudan din kansa akwai fargabar cewa bayan samun mulkin kai ranar 9 ga watan Yuli, zaman lafiya zai yi karanci.

Rahoton, wanda Kungiyar Kare Hakkokin Al'ummomi Marasa Rinjaye ta Kasa-da-kasa ta fitar, ya ce har yanzu kokawar samun albarkatun kasa tsakanin kabilun yankin na haifar da tashe-tashen hankula.

Kudancin Sudan din dai na da kabilu da dama, kuma rahoton ya ce kanana daga cikinsu na fuskantar wariya kuma ba su da wakilci a al’amuran siyasar yankin—a lokaci guda kuma ana karkatar da arzikin kasa ga manyan kabilu.

Rahoton ya kuma yi kira ga gwamnatin Kudancin Sudan ta mayar da hankali wajen samawa kananan kabilu wakilci a gwamnati da kuma raba arzikin kasa cikin adalci.