Sojojin Syria sun yiwa garuruwa biyu tsinke

Shugaba Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Bashar al-Assad na Syria

Wata sanarwa daga rundunar sojin Syria ta tabbatar da rahotannin da masu fafutuka suka bayar cewa sojoji da tankokin yaki sun yiwa wadansu garuruwa biyu tsinke.

Garuruwan dai suna kan babbar hanyar motar da ta hade babban birnin kasar ne, wato Damascus da kuma birni na biyu mafi girma, wato Aleppo, wanda ke arewacin kasar.

A daidai lokacin da ta ke amfani da karfin soji don maido da ikonta a arewaci kuma, gwamnatin kasar ta Syria ta nace cewa tana daukar matakan kawo sauyi.

A wani mataki da ake ganin yunkuri ne na rarrashin al'umma, daya daga cikin mawadatan kasar, Rami Makhlouf, ya ce zai yi watsi da harkokinsa na kasuwanci.

Shi dai Rami Makhlouf yana cikin mutanen da masu zanga-zanga a kasar ta Syria suka tsana.

Kuma lokacin da aka fara bore a garin Deraa a watan Maris, wurare na farko da aka farwa sun hada da gine-ginen kamfanin wayar salula na Syriatel, wanda ta hanyarsa Mista Makhlouf ya zama hamshakin mawadaci.

Yanzu dai ya ce zai sadaukar da dukiyar da ya samu ta hanyar kamfanin ga ayyukan taimakon al'umma; sannan shi kansa zai koma ayyukan agazawa al'umma.

Rami Makhlouf, wanda dan uwa ne ga shugaban kasar, yana cikin mutanen da ke juya akalar mulkin kasar, kuma wadannan kalamai na shi sun nuna irin matsin lambar da gwamnati ke sha.

Sai dai watakila wannan mataki ya zo a makare, saboda a cewar daya daga cikin shafukan sada zumunta na intanet mallakar jagororin zanga-zangar, ba abin da zai burge su illa a gurfanar da Mista Makhlouf da sauran wadanda suka ce sun wawashe dukiyar kasar a gaban kuliya.

A halin da ake ciki kuma, gidan talabijin na gwamnati ya nuna hotunan bidiyo na sojojin kasar sun yiwa garin Ma'arrat an-Nu'man tsinke.

Gidan talabijin din ya kara da cewa sojojin sun kuma nufi wani garin na biyu mai suna Khan Shaikhun, don hana wadanda ya kira kungiyoyin 'yan ta'adda rufe babbar hanyar.

Karin bayani