'Yan Syria na cigaba da shiga Turkiyya

Wasu 'yan Syria suna tsallakawa cikin Turkiyya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu 'yan Syria suna tsallakawa cikin Turkiyya

Pira ministan Turkiyya, Recep Erdogan ya ce ba zai rufewa 'yan gudun hijirar dake tsallakawa cikin kasarsa daga Syria kan iyakar su ba,yayin da daruruwansu ke gujewa fadan da ake yi a kasar.

Mr Erdogan ya ce a halin da ake ciki batun a rufewa 'yan gudun hijirar dake zuwa daga Syria kan iyakar Turkiyya ma bai taso ba.

Ya ce yana sa ido kan abin da ke faruwa a kasar ta Syria cikin damuwa, ya kuma yi kira ga shugaba Bashar al Assad da ya gudanar da sauye sauye a kasar.

Masu aiko da rahotanni sun ce 'yan gudun hijirar na tserewa ne daga garin Jisr al- Shugur inda ake sa ran sojojin gwamnati za su kai farmaki, biyo bayan ikirarin da gwamnatin kasar ta yi cewa a garin ne aka kashe ma ta jami'an soja da na 'yan sanda su fiye da dari da 20 a farkon wannan makon.