Obama ya yi mana bayani -'Yan Republican

Shugaban Majalisar Wakilai John Boehner Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Majalisar Wakilai John Boehner

’Yan jam'iyyar Republican a Majalisar Dokokin Amurka sun yi kira ga Shugaba Obama ya yi musu bayanin sahihanci a shari’ance na shigar sojojin Amurka cikin rikicin Libya.

Kakakin Majalisar Wakilai, John Boehner, ya ce gwamnatin Obama na gab da keta dokar wa'adin kwanaki sittin din da shugaban kasar ke da su kafin ya nemi amincewar majalisa game da amfani da matakin soji.

Sai dai fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce za ta mayar da martani kafin karshen wa'adin, wanda ake sa ran zai cika ranar Lahadi mai zuwa.

’Yan jamiyyar Republican sun bayar da goyon bayansu ga shigar kungiyar tsaro ta NATO Libya, sai dai suna ganin an yiwa rawar da Amurka ke takawa a can mummunar fassara.