Masana sun maida martani akan sulhu da Boko Haram

boko haram
Image caption Shugaban 'yan Boko Haram wanda aka kashe Muhammed Yusuf

A Najeriya, masana harkokin tsaro sun fara tsokaci dangane da furucin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yi na cewa yana goyon bayan a tattauna da kungiyar Boko Haram, wadda ake zargi da kai hare-hare a yankin arewacin kasar.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a wajen wani taro kan cutar HIV da ke gudana a birnin Washington na Amurka.

Magoya bayan kungiyar ta Boko Haram sun ce suna son a kaddamar da tsarin shari'ar Musulunci a kasar.

A baya ma dai 'yan kungiyar sun yi watsi da tayin da sabon gwamnan jihar Borno ya yi musu na tattaunawa domin kawo karshen hare-haren da suke kaiwa.

Hare-haren da magoya bayan kungiyar ke kaiwa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da suka hada da malaman addini, sarakunan gargajiya, da ma jami'an tsaro.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya shaida wa manema labarai cewa, babu gwamnatin da za ta so ta kashe 'yan kasar ta, ko da kuwa sun dauki makamai don yakar ta.

Alhaji Ibrahim Babankowa tsohon kwamishinan 'yan sandane a Najeriya kuma kwararrene a harkokin tsaron cikin gida yace akwai jan aiki a gaban hukumomin kasar wajen yin silhu da 'yan Boko Haram.