Yaushe ya kamata a fara baiwa jariri abinci mai nauyi?

Yaushe ya kamata a fara baiwa jariri abinci mai nauyi?
Image caption Akwai rudani kan ainahin lokacin da ya kamata a fara baiwa jarirai abinci mai nauyi

Shekaru goma da suka wuce, Hukumar Lafiya ta Duniya ta wallafa wani rahoto inda ta shawarci iyaye mata da kada su fara baiwa jariransu abinci mai nauyi har sai bayan wata shida.

A maimakon haka su ci gaba da basu nono. Amma wasu kungiyoyin likitoci a Burtaniya sun yi watsi da wannan shawarar.

Suka ce dadewa kafin fara bai wa jarirai abinci ka iya yin illa ga lafiyarsu.

Binciken na su ya haifar da cecekuce a Burtaniya, inda wasu masanan ke goyon bayan shawarar da ake da ita ta asali. To ko shayarwa ita ce ta fi wajen shayarda yara?

Fiye da shekaru goma kenan masana suka shawarci iyaye da ke shayarwa da su maida hankali wajen shayar da jarirai da nononsu na asali har watanni shida.

A cewarsu shi ne abincin da ya fi dacewa da kananan yara saboda yana dauke sinadarai masu gina jiki, su kuma karesu daga cututtuka kamar mura da amai da gudawa.

Sabon bincike

Sai dai wata tawagar likitocin Burtaniya ta nuna shakku kan wannan shawara. Sun yi nazari kan wasu alamu - sannan suka ce watanni 6 ya yi yawa ga wasu jariran ace basu fara cin abinci mai nauyi ba - domin za su iya gamuwa da matsaloli.

Dr Marie Fewtrell ita ce ta jagoranci binciken a jami'ar University College da ke London:

"Abu ne da yake a zahiri cewa wasu jariran da ke da watanni 4 zuwa 6 abinci ba zai ishesu ba saboda suna girma - akwai rudani kan lokacin da hakan zai faru saboda ya banbanta daga yaro zuwa yaro".

Amma kungiyar kwararru ta unguwar zoma a Burtaniya ta yi watsi da binciken.

Suka ce wasu daga cikin jariran ba za su iya daukar abinci mai nauyi ba idan ba su kai watanni shida da haihuwa ba.

Ta kuma yi gargadi kan baiwa jarirai abinci mai zaki domin a cewarta - zai sa yara su saba da cin abinci bakai ba gindi.

Virginia Howes wacce unguwar zoma ce a garin Kent a Ingila na da wata damuwar daban:

"Idan muka fara bada wani abincin daban to zai haifar da matsala kan nonon da iyaye ke baiwa jariransu - shayarwa ce da ta dogara kan bayarwa da kuma bukata".

An samu daidaito a wani wuri

Ma'aikatar lafiya ta Burtaniya ta nace cewa nonon uwa na dauke da dukkan ababan gina jiki da jarirai 'yan kasa da wata shida ke bukata - amma ta yi alkawarin nazari kan duk wani sabon bincike.

Duk da wannan cece-kucen da ake yi, Hukumar lafiya ta duniya ta ce kimanin kashi 60 cikin dari na iyaye mata a duniya, ba sa kai watanni shida suna shayar da jariransu.

Wasu kan fara ba su abinci mai karfi - yayin da wasu ke amfani da madarar gari.

Inda aka samu daidaito shi ne na baiwa matan da ke zaune a kasashen da babu tsaftataccen ruwa.

Koda 'yan Burtaniyan da suka gudanar da binciken na baya-bayan nan, sun amince cewa a irin wadannan yankuna mata kan ci gaba da shayar da jariransu har wata shida - saboda zai yi wuya a yi wanke-wanke a dafa abinci ba tare watsuwar kwayoyin cuta ba.