Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Fuskantar damuwa ga mai ciki ko jego

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Mata masu ciki da jego na fama da fargaba

A cewar Hukumar Lafiya ta Burtaniya NHS matsananciyar damuwa da wasu masu jego kan shiga zai iya shafarsu ta hanyoyi da dama.

Kuma alamun hakan na bayyana da zarar mace ta haihu, inda masu wannan matsala kan kwashi watanni ko ma a wasu lokutan sama da shekara daya kafin su samu lafiya.

Hukumar ta kara da cewa iyaye mata da dama basa sanin cewa suna fama da wannan matsala kuma ba sa gayawa 'yan uwa da abokan arziki irin halin da suke ciki.

Saboda haka yake da muhimmanci mai gidan da iyali da abokai su san alamomin cutar don a nemi shawarar kwararru a fannin kiwon lafiya da wuri.

To fadawa cikin tsananin damuwa na daga cikin jerin wasu matsaloli na kiwon lafiya dake barazana ga mata masu juna biyu ko wadanda ke shayarwa.

Kuma akan wannan batun ne shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa ya tattauna da Dr. Mairo Mandara wata kwarrariyar likitar mata da ke Abuja a Najeriya.