ICC na tuhumar sojojin Gaddafi da fyade

gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kanar Mu'ammar Gaddafi na Libya

Babban mai shigar da kara da kotun laifufukan yaki na duniya wato ICC ya ce yana kara gamsuwa akan cewar Kanar Gaddafi na amfani da fyade akan mata a matsayin wani makami akan masu adawa da shi.

Lius Moreno Ocampo ya ce ma'aikantanshi na binciken hujjojin dake nuna cewar Shugaban Libyan din na baiwa Sojojinsa maganin kara karfin maza.

Tuni dai Ocampo ya bukaci alkalin kotun na ICC su tuhumi Kanar Gaddafi akan laifin jin zarafin bil adama

Babban mai shigar da kara na ICC din ya shaidawa manema labarai cewar yana bincikinen rahotanni fyade kuma musamman yana kokarin kafa hujja ko daga sama ne aka bada umurnin aci zarafin matan ko kuma sojojin suna yin haka ne don kashin kansu.

Lius Moreno Ocampo yace hujjoji na nuna cewar Kanar Gaddafi na goyon bayan yin fyaden a matsayin wani makami na waki har ma yana baiwa sojojinsa maganin kara karfin namaji wato Viagra don sojojin su kara azama.

Mr Ocampo yace yana da anniyar tabbatar da ainihin gaskiyar lamarin abinda ya kira sabon salon gallazawa mutane a Libya.

Babban mai shigar da karan yace matakila ya bukaci ICC ta tuhumi Kanar Gaddafi akan batun goyon bayan fiye idan har aka tabbatar da laifin.

A watan daya gabata ne Mr Ocampo ya bukaci alkalan ICC su bada sammacin kama shugaban Libya da dansa da kuma shugaban leken asirin Libya, bayan ya zargesu da aikata laifukan cin zarafin bil adama ta hanyar kashewa da kuma zaluntar masu zanga zangar kin jinin gwamnati.