Dakarun Syria na ci gaba da kai hari Jisr al Shugour

Dakarun Syria na ci gaba da kai hari Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Lahadi ne dakarun Syria suka sake kwace garin Jisr al Shughour

Masu fafutuka a Syria sun ce dakarun gwamnati a kusa da kan iyakar Turkiyya na kai hari kan wasu garuruwa kusa da Jisr al Shughour, inda gwamnati ta karbe ranar Lahadi.

Suka ce dakarun na nufar garin Maarat an-Namaan inda gidan talabijin na kasar ya ce ana kaiwa gine-ginen gwamnati da na jami'an tsaro hari a 'yan kwanakin nan.

Lamarin na zuwa ne lokacin da 'yan gudun hijirar da ke kauracewa rikicin na Libya ke kara tururuwa zuwa Turkiyya.

Rahotanni sun ce akalla mutane dubu bakwai ne suka tsallaka iyaka daga Syria zuwa kasar Turkiyya.

Haka kuma akwai wasu da dama da ke neman mafaka a filin Allah Ta'ala a bangaren iyakar Syria.

Shugaban Amurka Barack Obama ya sake kira ga shugaba Bashar al'Assad ya yi murabis idan ba zai iya jagorantar sauye-sauyen dimokuradiyya ba.