'Yan Syria na tururuwa zuwa Turkiyya

Fira Ministan Turkiyya Tayyib Erdogan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fira Ministan Turkiyya Tayyib Erdogan ya ce ba zai rufe kan iyakar kasar ba

Ana kara samun 'yan kasar Syria da ke tururuwa zuwa Turkiyya, a daidai lokacin da ake hasashen sojoji za su kaddamar da hari a garin Jisr al-Shughour.

Akalla mutane 1,000 ne suka tsallaka iyakar kasar zuwa Turkiyya a daren jiya, abinda ya kai adadin zuwa 1,600.

Fafaroma Benedict da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga Syria da kada ta kai hari kan jama'arta.

Kiran ya zo bayan da Faransa da Burtaniya suka shirya wani kuduri da zai nemi Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da yadda Syria ke muzgunawa masu zanga-zanga.

Sai dai Rasha ta ce ba za ta goyi bayan kudurinba tun kafinma a gabatar da shi domin kada kuri'a.

Jami'an tasaro ma sun mutu

Ana tunanin kai hari a garin Jisr al-Shughour ne domin mayar da martani ga abinda jami'an gwamnati suka bayyana da kisan jami'an tsaro 120 da wasu 'yan gwagwarmaya suka yi a can.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yan gudun hijirar na zaune ne a wani sansani na Red Crescent

Ta ce mazauna garin sun nemi dauki da sojoji domin maido da doka da oda.

Amma masu fafutukar kare hakkin bil'ada sun ce fadan ya barke ne bayan da sojoji suka bude wuta kan masu zanga-zangar lumana.

Jami'an Turkiyya na tantamar hanyoyin da za su bullowa lamarin. 'Yan sanda na hana 'yan jarida tattaunawa da 'yan gudun hijirar, wadanda yawancinsu ke zaune a sansanin Red Crescent wanda ke cike da jami'an tsaro.

Mazauna Turkiyya, wadanda yawancinsu dangi ne ga 'yan Syria, sun san lokaci da kuma inda jama'a za su tsallaka iyakar saboda suna magana ta wayar salular da ke dauke da layukan Turkiyya.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce fiye da mutane 1,000 ne aka kashe tun bayan fara zanga-zangar adawa da mulkin shugaba Bashar al-Assad, kuma a yanzu akwai alamun daruruwan jami'an tasaro ma sun mutu.