Hukumar kare hakkin bil Adama ta yi tir da Syria

Navi Pillay Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An soma yi wa Syria kofar raggo

Shugabar Hukumar kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga gwamnatin Syria da ta dakatar da abin da ta kira munanan matakan da take dauka na murkushe masu zanga-zanga.

Tana magana ne yayin da wasu karin 'yan gudun hijirar Syria suka tsallaka cikin Turkiya, domin guje wa abin da suke fargabar cewa wani mummunan farmaki ne gwamnati ke shirin kaiwa a arewacin kasar.

Mrs Pillay ta ce mai yiwuwa an kashe mutane fiye da dubu daya da dari daya, aka kuma kama wasu karin dubbai, tun daga lokacin da aka fara tashin hankali a kasar ta Syria a cikin watan Maris.

A waje daya kuma, hukumar dake sa ido kan makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, ta yanke shawarar gurfanar da Syria a gaban Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniyar game da shirin nukiliyar da ake zargin tana da shi a boye.

Hukumar makamshin Nukiliyar ta duniya, IAEA, ta kada kuri'ar gurfanar da Syria a kan ikirarin wata tashar nukiliyar da ba a bayyana ba a kusa da Deir Alzour a can cikin yankin arewa maso gabacin kasar.

Isra'ila ce dai ta lalata tashar da ake zargin, wadda Syria ta hakkake cewar wuri ne na soji marassa nasaba da Nukiliya, a shekara ta dubu 2007.

Amurka da kawayenta na yammacin duniya ne dai suka jagoranci kudurin.

Rasha da China, muhimman wakilan kwamitin sulhun ba su goyi bayan yunkurin ba.

Matakin na hukumar makamashin nukiliya ta duniya ya zo ne yayinda matsin kasasehn duniya ke karuwa a kan Kwamitin sulhun MDD da ya hukunta Syria game da murkushe zanga zanga da karfi.