NATO na neman agajin kasashenta

Sakataren tsaron Amurka , Robert Gates, ya ce kungiyar tsaro ta NATO na kasadar zama wani gungun soji maras muhimmanci muddun dai wakilanta na turai ba su kara kudaden da suke kashewa kan harkokin soji ba.

A cikin wani kwakkwaran jawabi gabanin murabus dinsa nan gaba a cikin watan nan, Mr Gates ya ce yake - yaken da kungiyar tsaron ta NATO ke jagoranta a Afghanistan da Libya sun fito da babban rauni ta fuskar karfin soji da kuma aniyar siyasa ta wasu kawayen kungiyar. Ya ce, yayinda kowace kasa wakiliyar kawancen ta kada kuri'ar amincewa da yakin Libya, kasa da rabi ne suka shiga cikinsa, kuma kasa da kashi daya cikin 3 keda aniyar shiga cikin yakin.

Mr Gates ya ce Amurka ba za ta ci gaba har sai abinda hali yayi da daukar nauyin harkar tsaron dake karuwa sakamakon zabtare kudade kan sha'anin tsaro da ake yi a Turai ba.