Ra'ayi Riga: Tasirin dokar yaki da ta'addanci a Najeriya

Gawawwakin 'yan Boko Haram
Image caption Wane irin karo dokar ta yi da addini da al'ada?

A wannan makon ne shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya sa hannu kan dokar yaki da ta'adanci da kuma halatta kudaden haram. Sai dai ra'ayi ya bambanta a kasar game da yadda za a aiwatar da wannan doka.

To ko wane irin tasiri ne wannan doka za ta yi wajen yaki da ta'addanci da kuma halatta kudaden na haram?

Batun ta'addanci dai batu ne da ke da tsawon tarihi, kuma ya samo asali ne daga gwagwarmaya tsakanin kungiyoyi ko kuma gwamnatoci, wadanda suke kokarin yakar danniya, ko kuma cimma wata manufa ko akidar da suka yi imani da ita.

An sami kungiyoyi da dama a cikin karni na ashirin, wadanda aka yiwa lakabi da kungiyoyin ta'addanci, irinsu kungiyar ETA ta kasar Spain, da kuma kungiyar IRA ta arewacin Ireland, sannan a baya bayan nan kungiyar Alqa'ida, wadda ake ganin cibiyarta na Afghanistan, da kuma rassa a wasu kasashe.