Sosojin Syria sun afka Jisr al-Shugur

Sojojin Syria
Image caption Sojojin Syra sun afkawa garin Jisr al-Shugur

Sojin Syria sun afkawa garin Jisr al-Shughur, bayan da suka lashi takobin daukar fansa game da abinda suka ce kashe jami'an tsaro dari da ashirin da akai a garin a farkon wannan makon.

An bayyana a shafukan yanargizon yan adawa cewa an ji amon bindigogi a yankin, kuma gwamnati ta ce farmakin nada nufin maido da tsaro a garin .

Gidan talabijin na kasar ya ce yan bindiga sun cunna wuta a kan kayan gona da itatuwa domin rage hanzarin dannawar da sojin ke yi zuwa gaba.

Ana jin cewar galibin jama'a dai sun bar garin.

Sai dai yan sa'o'in da suka wuce wani mazaunin garin wanda ya ce bai samu damar barin garin ba, ya ce ya ga tankokin yaki suna bude wuta barkatai a kan fararen hular da ba sa rike da ko da tsinke.