Syria na kokarin tabbatarda doka da oda

syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata mai zanga zanga a Syria

Kafar talabijin na kasar Syria ta ce dakarun sojin kasar sun fara aikin dawo da doka da oda a birninda aka halaka sojojinta dari da ashirin a farkon wannan mako.

Kafar ta ce an kaddamar da irin wannan aiki a kauyukan dake kewaye da birnin na Jisr Al-Shughur, domin kama yan bindiga.

Da farko dai mazauna birnin sun shaidawa BBC cewa gwamnatin syria na hukunta su.

Wakilin BBC ya ce "an garzaya da wata matashiyar yarinya dake fama da cutar koda zuwa asibiti, inda aka kore ta. Daga bisani an fita da ita zuwa kasar Turkiyya domin samun kulawar gaggawa".