Sabon luguden wuta da bindigogin atilare a kan Misrata

Likitoci a garin Misrata mai tashar jiragen ruwa, sun shaidawa BBC cewa mutane akalla talatin da daya ne aka kashe, aka kuma raunata wasu sama da dari da hamsin, a wani mummunan farmaki da dakarun Kanar Mu'ammar Gaddafi suka kai da bindigogin igwa.

Sun ce shi ne hari da ba kakkautawa mafi muni da aka kai wa garin, tun bayan da 'yan tawaye suka kwace iko da shi.

Wani wakilin BBC a Misrata ya ce , kusan a ce birnin na fada na na kwatar kansa.

A halin da ake ciki, Pirayim raministan Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya shiadawa gidan talabijin na Turkiyya cewa, yayi ma Kanar Gaddafi tayin ba shi kariya, idan zai fice daga Libyar, Turkiya za ta taimaka ma sa ya tafi duk inda yake so.

Mr Erdogan ya ce bai samu wani martani kan tayin nasa ba.