Matsalar safarar miyagun kwayoyi a Mexico

Felipe Calderon
Image caption Ana jerin-gwano a Mexico

Daruruwan mutane sun yi jerin-gwano a Mexico, domin jimamin mutanen da suka mutu sakamakon tashe-tashen hankulan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi.

Masu jerin-gwanon dai sun yi tafiyar kilomita 2,500, kuma ana sa ran za su sanya hannu akan wata takarda da ke nuna kyamar tashin hankali a garin Ciudad Juarez, da ke kan iyakar kasar da Amurka.

Kusan mutane dubu arba'in ne dai aka kashe a kasar, tun bayan shugaba Felipe Calderon ya kaddamar da yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a shekara ta 2006.

Masu jerin-gwanon, na son gwamnati ta daina fafatawa da masu fataucin miyagun kwayoyin, sai dai gwamnati ta ce ba za ta daina ba.