An kashe wani jagoran Al-Qa'ida a Somaliya

Fazul Abdullah Mohammed
Image caption Fazul Abdullah Mohammed

An kashe jagoran kungiyar Al-Qaeda reshen gabashin Afurka, Fazul Abdullah Muhammed a wata musayar wuta da aka yi a Mogadishu, babban birnin Somalia.

Gwamnatin rikon kwaryar Somaliyan ta ce, an kashe Fazul Muhammed ne tun a farkon makon jiya, kuma gwajin kwayoyin halitta na DNA ya nuna cewa hakika shi din ne.

Sakatariyar harkokin wajen Amurkar, Hillary Clinton, ta bayyana kisan da cewar, babban koma-baya ne ga Al-Qaeda.

Wani babban jami'i ma sashen tsaron kasa a Somalia ya ce an kashe Fazul Abdullah Mohammed ne tare da wani mutum a Mogadishu da daren ranar talata.

Sai dai kakakin rundunar kiyaye zaman lafiya ta tarayyar Afrika a Somalia, ya ce ga alama hoton gawar bai yi kama da Fazul Abdullah Mohammed ba.

Haka nan kuma Kungiyar masu tayar da kayar bayan Islama ta Al shabab, ta ce rahotannin mutuwarsa ba gaskiya ba ne.

A baya dai, Amurka ta saka ladan miliyan biyar ga duk mutumin da ya bata bayanan da za su sanya a kama shi.