Dubban mutane sun gudu daga Syria zuwa Turkiya

Jami'an Turkiyya sun ce mutane sama da dubu hudu ne a yanzu suka tsallaka kan iyaka suka shiga kasar daga Syria, domin tsere ma tashin hankalin da ake yi a can.

'Yan kasar ta Syria sun fi tserewa ne daga wani yanki a arewaci, inda wani ganau, ya shaidawa BBC cewa , a jiya Juma'a, sojoji sun kai farmaki da tankokin yaki, inda suka kashe jama'a.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da labarin.

Metin Corabatir, shi ne kakakkin hukumar kula da yan gudun hijira a Turkiyya, ya ce , "sansani na biyu ya fara tsugunar da mutane dubu biyu a kan iyaka. Kungiyar agajin Red Crescent ta Turkiya a yanzu tana kafa sansani na uku, inda za a tanaji tantuna dubu daya, domin tsuganar da mutane dubu biyar."