Yau ake bikin ranar 'June 12' a Najeriya

Wata mace na kada kuri'a a zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yau ake bikin ranar 'June 12' a Najeriya

A Najeriya, yau ake bikin ranar sha biyu ga watan Yuni, domin tunawa da zaben shugabancin kasar da aka gudanar a shekarar 1993, wanda ake ganin marigayi Cif Moshood Abiola ne ya lashe.

Ita dai gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin ta soke zaben, wanda akasarin 'yan kasar ke ganin shi ne mafi inganci a tarihin siyasar kasar.

Jama'a da kungiyoyin da ke ikirarin kare mulkin dimokaradiyya sun mayar da bikin wannan rana a matsayin wata al'ada.

Najeriya dai ta yi fama da fadace-fadacen siyasa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.