Dakarun Syria sun yi wa garin Jisr al-Shughuor dirar mikiya

Dakarun Syria a kusa da  garin Jisr al-Shughur Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Syria a kusa da garin Jisr al-Shughur

Dakarun Syria sun kaddamar da harin a yi-ta-ta-kare a kan garin Jisr al- Shughour, dake arewa maso yammacin kasar, a matakin baya baya na kokarin murkushe ma su bore.

Wasu 'yan tawaye sun ce sojojin sun yi amfani da tankokin yaki, da bindigogin iggwa da kuma jiragen yaki masu saukar angulu.

Gidan talabjin na Syria ya ce an fafata da wasu 'yan bindiga da suka ja daga.

Ita dai gwamnatin Syria na cewa tana kai farmakin ne a kan 'yan bindigar da take zargi da kashe sojojinta su dari da ashirin a Jisr al Shughour ranar Litinin.