Erdogan zai fara sabon wa'adin mulki na uku a Turkiya

Pirayim Minista Erdogan na Turkiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Pirayim Minista Erdogan na Turkiya

Pirayim Ministan Turkiya, Tayyip Erdogan zai soma wa'adin mulki na uku, bayan jam'iyyarsu ta AKP ta lashe zaben kasar da aka gudanar ranar Lahadi.

Jam'iyyar dai ta lashe kusan kashi hamsin ne na kuri'ar da aka kada a zaben, kana kuma ta samu rinjaye a majalisar dokoki, amma rinjiyen bai kai ya ba shi damar aiwatar da sauyi ga kundin tsarin mulkin kasar ba.

A cikin jawabin amsar nasararsa, ya shaidawa magoya bayansa da ke cike da farin ciki cewar zai mayar da hankali a kan samun haduwar baki da kuma sulhuntawa.

Masu sukar Mista Erdogan sun ce aniyarsa ita ce ya tsawaita wa'adin ikonsa.

Wakilin BBC a Santanbul ya ce nasarar Pirayim Ministan ta sa ya zama Shugaban Turkiya mafi karfin iko tun bayan mutumin da ya kirkiro kasar, Ataturk.